Ɗan tajarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Kwankwaso ya raba kayayyaki ga marayu tare da bayar da tallafi ga marasa lafiya a wasu asibitoci.

Kwankwaso ya yi hakan ne a wani ɓangare na bikin cikarsa shekaru 66 a duniya.

Sanata Kwankwaso ya raba kayayyaki ga marasa karfi a wasu sassa na jihar Kano.

Shugaban kwamitin jin ƙai na Kabiru Getso ya ce daga cikin kayayyakin da aka raba akwai kayan sakawa, da sauran kayan amfani.

An raba kayayyakin karƙashin gidauniyar Kwankwansiyya kamar yadda wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa ta nuna.

Sannan gidauniyar ta bayar da tallafi a wasu maƙabartu na jihar Kano, daga ciki akwai maƙabartar Tarauni, Maƙabartar Ɗandolo da wasu mazauna gidan gyaran hali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: