Wata Babbar kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa sauya wa alkalai 21 guraren aiki a fadin Najeriy bashi da wata alaka da hukuncin da kotun ta yanke na sakin wadanda ake zargi da aikata ta’addanci karkashi jagorancin Nmadi Kanu.

Babban rijistaran kotun Malam Umar Muhammad Bangari ya bayyana cewa labaran da wasu kafofin yada labaran su ke yadawa cewa wasu alkalai uku da suka yanke hukunci a ranar 13 ga watan Oktoba da su saki Nmadi Kanu dukkan su an canja musu gurin aiki.
Rijistaran ya kara da cewa Alkali daya ne daga cikin Alkalai uku da su ka gudanar da shari’ar Nmadi Kanu aka rage masa matsayin da ya ke dashi.

Malam Umar ya ce ba sabon abu bane sauya wa Alkalai gurin aiki wanda ana yin hakan ne domin kara samun kwarewa.
