Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa ya bi dukkan wasu hanyoyin da su ka dace wajen sabunta wasu kudade da ake amfani da su a Najeriya.

Mai magana da yawun babban bankin Osita Nwanisobi ya bayyana hakan a lokacin da ya ke mayar da martani ga ministar kasafi da tsare-tsare Zainab Shamsuna Ahmad wadda ta ce ma’aikatar ta bata da masaniya akan sabunta kudaden da za a yi.

A jiya Juma’a ministar kasafin ta isa ga kwamitin majalisar wakilai tare da kin amincewa da lamarin inda ta ce ba a wannan lokacin ya kamata ‘yancin yazo ba.

Hakan ne ya sanya kakakin babban bankin ya nuna mamakinsa akan furucin na ministar inda ya ce babban bankin ya aikewa da shugaban kasa Buhari takardar sauya kudaden inda ya amince da hakan.

Osita yayi bukaci ‘yan Najeriya da su amince da kudurin sauyin kudaden inda ya ce zai amfani ‘yan kasar baki daya.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun boye kudade masu tarin yawa ba a asusun bankunan ‘yan kasuwa ba.

Kazalika ya ce har kawo yanzu yanayin kula da kudade a Najeriya ya na fuskantar kalubale wanda hakan ke barazana ga nagartar kudaden bankin na CBN da kasar baki daya.

Osita ya kara da cewa Bankin na CBN yayi hakuri na tsawon lokuta masu yawa kawo yanzu shekaru 20 kenan ba a sake tsarin fasalin kudaden ba wanda ya dace a dinga sauyawa duk shekaru biyar zuwa takwas.

Kakakin bankin ya ce sake tsarin wasu kudaden aiki ne na babban bankin ba dan wasu kungiyoyi ba wanda hakan zai assasa tare da takaita amfani da tsabar kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: