Hukumar hana sha da fataucin migaun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta kama wani mai unguwar Gidan Abba a ƙaramar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
An kama Abubakar Ibrahim tare da wasu mutane 38 bayan an samesu da kayan maye daban-daban.
Mai magana da yawun hukumar ta kasa Femi Babafemi ne ya sanar da haka yau a Abuja babban binrin tarayyar Najeriya.
Ya ce jami’ansu sun kama wasu kayan maye a filin tashi da saukar jiragen sama a Murtala Muhammed da ke Legas yayin da aka shigo da su ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wato Dubai da ƙasar Pakistan.
Ya ƙara da cewa jami’ansu sun kama kayan maye daban-daban a tsakanin jihohi Bakwai na Najeriya.
Sannan an kama mutane 38 da kuma wani mai unguwa a jihar Sokoto.