Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kadarorinsa bayan ya ci gaba da fuskantar matsi daga ƴan kasar.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin kungiyar NAPOC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa yana da gidajen gas biyu a birnin Landan.
A cewar tsohon gwamnan na jihar Lagas, matarsa Remi ita ce ke kula da gidajen man wanda daga bisani ya siyar da su domin daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).

Bayanin Tinubu kan tushen arzikinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa tsohon gwamnan ya yi wasu badakaloli kafin a sanshi a matsayin dan siyasa.

Da yake ci gaba da jawabi, Tinubu ya bayyana cewa shi ya dauki nauyin NADECO tare da Alfred Rewane duk da cewar ya dade da mayar da hankali wajen zuba jari a kasuwanci daban-daban kafin ya shiga harkar siyasa.