Rahotanni daga laramar hikumar maradun a jihar Zamfara sun nuna cewar wasu ƴan sa kai sun samu nasarar hallaka yan bindiga biyu a jihar.

Al’amarin ya faru a yau yayin da ake tsaka da cin kasuwa a garin Gidan Goga garin da ke maƙobtaka da Ƙauran Namoda.
Tun da farko yan bindigan sun shiga kasuwar Gidan Goga tare da nufin kai hari.

Sai dai jami’an sa kai sun samu nasarar daƙile harin tare da kashe biyu daga ƴan bindigan.

Sai dai rahotanni sun nuna cewar yan bindigan sun hallaka mutane uku.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewar, ƴan binddigan sun yi wa kasuwar ƙawanya tare da nufin aikata ta’addanci.
Yayin da aka tuntuɓi kakakin ƴan samda a Zamfara bai samu amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin haɗa rahoton.