Daga Mansur Umar

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa a Najeriya ASUU da takwararta wato CONUA sun bayyana bacin ran su, biyo bayan karbar rabin albashi a matsayin albashin aikin watan oktobar da ya gabata.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU Chris Piwuna ya tabbatar mata da hakan a daren jiya Alhamis, inda ya bayyana matakin a matsayin “Cin mutunci, wulakantawa da kuma abin kunya”.

Sannan shi ma babban jami’in kungiyar CONUA Na kasa Niyi Sunmonu ya bayyana matakin a matsayin abin rashin jin dadi, sannan ya hakurkurtar da mambobin kungiyar da cewa za’a shawo kan matsalar komai ya daidaita.

Idan za’a iya tunawa kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ASUU ta tsunduma yajin Aiki ne tun 14 ga watan Fabarairun da ya gabata, kuma bata bayyana janye yajin aikin ba sai a 14 ga watan Oktoba Na shekarar da muke ciki, biyo bayan umarnin da kotun da’ar ma’aikata ta bata Na cewa ta janye yajin aikin.

Bayan da ta shafe tsawon watanni bakwai tana yin yajin aikin.

A lokacin da suke sanar da janye yajin aikin shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa, bayan biyayya ga umarnin da kotun ta basu Na janye yajin aikin, sun janye sakamkon shiga cikin al’amarin da kakakin majalissar wakilai ta ‘kasa Femi Gbajabiamila yayi a maimakon malaman jami’ar.a

Sannan ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da a cimma sahihiyar matsaya da kungiyar malaman jami’o’in akan albashin su da ba’a biya su ba Na watannin da suka shafe suna yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: