Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano ta yi tir da dukan wani dan jarida da ake zargin dan Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa ya yi a jihar.

Sanarwar da shugaban ƙunsgiyar a Kano, Abbas Ibrahim da sakatarenrta, Abba Murtala suka sa hannu sanarwar ta ce, duk da cewa batun na gaban kotu da rundunar ’yan sanda, ya yi fatan a yi binciken kwakwaf kan lamarin.

Ya ce suna tunatar da ’yan siyasa cewa, ’yan jarida da ’yan siyasa abokan juna ne ta fuskar kawo cigaba na samuwar ingantaccen mulkin dimokurdiyya a shekarar 2023.

Sanarwar ta ce kyakkyawar dangantar da ke tsakanin Gwmanatin jihar Kano da ’yan siyasa da kuma ’yan jarida a yanzu babu kamarsa, kuma kauce wa hakan ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba.

Sannan kungiyar ta ce ita ma za ta kafa kwamitin mutum uku don yin wani kwarya-kwaryar bincike na daban domin gano gaskiyar lamarin.

Ana zargin dan majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa da naushin wakilin jaridar Leadership a gidansa yayin wata hira da suka je yi da shi a farkon makon nan.

An ruwaito cewa dan majalisar ya fusata ne a lokacin da suke yi masa tambaya kan zargin da ake yi masa da jifan mataimakin dan takarar gwamnan jihar Kano na Jam’iyyar APC, Murtala Sulen Garo, ya ji masa ciwo a hannu yayin wani taro a gidan mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: