A yau Litinin ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, jigilar fasinjoji a jirgin kasa na hanyar Kaduna zuwa Abuja zai dawo a watan nan da muke ciki.

Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne shaidawa yan jaridu hakan, yayin da yake jawabi akan abubuwan da ma’aikatar sa ta cimma daga shekarar dubu biyu da sha biyar zuwa yanzu a birnin tarayya Abuja.

Idan za’a iya tunawa an dakatar da jigilar fasinjoji a hanyar ne, tun biyo bayan harin ‘yan ta’adda akan wani Jirgin kasa a ranar ashirin da takwas ga watan Maris na wannan shekarar da muke ciki.

Da yawa daga cikin fasinjojin Jirgin an yi garkuwa dasu bayan akalla mutum 9 da suka rasa rayukansu a yayin kai harin, kuma da yawan wadanda aka yi garkuwa da su din sun shafe watanni a hannun masu garkuwa dasu kafin daga bisani su shaki iskar yanci.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Ministan yana bayyana cewa ibtila’in da ke faruwa a hanyar abin bakin ciki ne, kuma da yardar Allah ba za’a kara fuskantar wani Abu makamancin haka ba.Dan kuwa mun dauki matakan da suka kamata.

Ya kara da cewa a watannan na Nuwamba zamu dawo aiki a wannan hanyar kamar yadda na fada a baya cewa, ba zamu dawo aiki ba har Sai duk wadanda suke tsare a hannun yan ta’adda sun dawo cikin iyalan su lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: