Wata kotu a jihar Filato ta yankewa wani matashi mai shekara 20 huuncin zama a gidan gyaran hali saboda satar awakin mutane.

Kotun majistire da ke zamanta a Jos babban birnin jihar Filato ta tisa keyar matashin zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya ne bayan da ta kamashi da laifin da ake tuhumarsa da shi.

Da yake yanke hukuncin alkalin kotun mai shari’a Adam Sadiq ya baiwa matashin zabin biyan tarar naira 10,000 gami da biyan mai akuyar naira 40,000, a matsayin diyya.

Tun da fari dan sanda mai gabatar da kara Ibrahim Gokwat, ya bayyanawa kotun cewa wani mai suna Dung Gyang ne ya kai korafin ofishinsu dake Anglo Jos ranar 11 ga watan oktoba.

Ya kara da cewa bincikensu ya tabbatar wanda ake tuhumar ya haura gidan mai karar, ya kuma sace masa awaki biyu, da suka kai darajar naira 40,000, laifin da ya ce ya saba da sashe na 334 da kuma sashe na 271 na kundin laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: