Majalisar Dinkin duniya ta yi kiyasin yawan al’ummar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a tsakiyar watan Nuwamba da muke ciki.

Hukumar kula da yawan jama’a ta majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa al’ummar duniya za su kai biliyan takwas a ranar 15 ga watan Nuwamba, ta yi kiyasin cewa karuwar zata kasance ninki uku kenan na yawan al’ummar duniya na shekarar 1950, lokacin da ake da mutane biliyan 2 da rabi.

Jami’ar hukumar Rachel Snow ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa bayan karuwar da al’ummar duniya su ka yi cikin sauri a cikin shekara 1960, yanzu yana tafiyar hawainiya.

Yadda al’ummar duniya ke yaduwa ya ragu da kashi 2 da digo daya, a cikin shekarun 1962 da 1965 zuwa kasa da kashi 1 a shekarar 2020.

Saidai hukumar tayi wani hasashen daban dake nuni da cewa duba ga yadda ake samun karin tsawon rai inda ake kaiwa shekaru 72, da kuma karuwar wanda su ka kai minzulin haihuwa al’ummar duniya za ta cigaba da karuwa zuwa biliyan takwas da rabi a shekarar 2030.

Haka kuma hukumar ta yi hasashen al’ummar duniya za su kai biliyan tara da dubu dari bakwai a shekarar 2050, sannan a 2080 adadin zai kai biliyan goma da dubu dari hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: