Mahaifiyar wasu yara biyar da ‘yan
bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara watanni biyar da suka gaba ta nuna farin cikin ta sakamakon sakin ‘ya’yanta da ‘yan bindiga.

Matar a yayin bayyana sakin ‘ya’yan nata ta sanar da irin wahalar da ‘ya’yan nata suka fuskanta a lokacin da su ke hannun ‘yan bindigan.

‘Ya’yan da ‘yan bindigan su ka yi garkuwa da su ‘ya’yane ga wani tsohon babban akanta da ke Jihar ta Zamfara.

Bayan sace yaran mazauna Najeriya musamman Arewacin kasar sace yaran ya dauki hankulan mutane da dama.

Kafin sako yaran ‘yan bindigan sun saki wani faifan bidiyo dauke da manyan makamai ,inda sukayi barazanar hallaka su ko kuma su mayar da su yaransu matukar ba a biya su kudin fansa ba.

Maharan sun sako yaran ne a ranar Litinin bayan da rahotanni su ka nuna cewa sau uku mahaifin yaran ya na biyan kudin fansa.

Bayan shakar iskar ‘yanci da yaran su ka yi gwamnan Jihar ta Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya yi wata ganawa da yaran.

Mahaifiyar ‘yan matan hajiya Hadiza Abubakar ta shaidawa BBC cewa sunyi matukar farin ciki da aka sako ‘ya’yan nata.

Mahaifiyar yaran ta ce babban farin cikin da ta yi shine da ‘ya’yan nata suka shaida mata cewa ba a keta musu haddi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: