Kasashen Amurka da Birtaniya sun tsame Babban Birnin Najeriya, Abuja, daga cikin biranen da ake fargabar yiwuwar kai harin ta’addanci a Najeriya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Ofishin Kula da Harkokin Kasashen Waje na kungiyar Kasashen Rainon Ingila (FCDO) su ka fitar da sanarwar.

Sanarwar na cewa, Ofishin FCDO ya janye shawarar da ya ba ’yan kasashen waje a kan su guji ziyartar Abuja in ba ya zama dole ba.

Sai dai sanarwar ta ce gargadin da Ofishin ya yi na zuwa wasu garuruwa a Najeriya na nan daram.

Jihohin da ofishin ya gargadi ’yan kasashen wajen da ziyarta su ne, Borno da Yobe sai jihar Adamawa da Gombe sannan Kaduna da Katsina.

Sauran jiohin su ne Zamfara, da wasu jihohi biyu daga kudancin kasar da su ka hada da jihar Akwa ibom, da Cross River.

Jihohin da ke da sassaucin gargadi na FCDO sun hada da Bauchi, Kano da Jigawa sai  Neja da Sokoto.

Sannan akwai jihohin Kogi da kuma kilomita 20 daga bakin iyakar jihohin Neja da Kebbi.

Haka kuma  akwai jihohin Abia da Delta sannan Bayelsa sai Ribas da Filato da kuma jihar Taraba.

Ofishin ya kuma shawarci ’yan kasashen wajen da a kodayaushe su rika bincikar sashen da ke sa ido kan shige da fice, kafin su yi duk wata tafiya don ba su shawarwari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: