Hukumar kidaya ta kasa watau NPC tace mutane miliyan biyu za a dauka takaitaccen aiki a Najeriya domin suyi aikin kidayar ‘yan kasa a shekarar 2023.

Hukumar ta fara da jan-kunnen ma’aikatan da za a dauka cewa ka da suyi abin da zai bata mata suna kamar yadda sanarwar tazo a ranar Alhamis.

Duk wanda aka samu da laifi ko rashin gaskiya wajen aikin kidayar nan da za ayi, zai fuskanci fushin hukuma, za a hukunta har wanda ya tsaya masa.

Domin ganin an yi adalcin daidaita tsakanin jinsi wajen daukar aikin, Kwamishinan NPC na Ekiti, Ayodeji Ajayi yace mata za su samu gurabe akalla 40%.

Ayodeji Ajayi ya yi wannan bayani da ya zanta da manema labarai jiya Alhamis a garin Ado Ekiti.

kwamishinan na NPC yace mutane miliyan biyu aka yi tanadi domin su gudanar da wannan muhimmin aiki a badi.

Ajayi yace wadanda za su kirga adadin mutanen Najeriyan sun hada da asalin ma’aikatan NPC da wasu da za a dauka haya domin aikin wucin gadi.

Duk wani matashi da ya yi aikin da kyau, kuma aka ga kokarinsa, zai samu takardar shaida daga NPC wanda zai taimaka masa wajen samun aiki nan gaba.

Hukumar tana harin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi da sauran mutanen Najeriya masu nagarta da gaskiya domin cike guraben aikin da za a samu.

Rahoton yace za a bukaci malaman firamare, sakandare da manyan makarantu musamman kwararru a ilmin kasa da na halayyar ‘Dan Adam da kidaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: