Jami’an rundunar Sojin Operation Forest Sanity sun samu nasarar ceto wasu mutune da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Daraktan yada labaran rundunar ta tsaro Manjo Musa Danmadami ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce dakarun sun samu nasarar ne a ranar Alhamis a yayin wani sintiri da su ka fito har zuwa sannanin na ‘yan bindiga a kauyen Danmarke da ke karamar hukumar Gummi ta Jihar.

Musa Danmadami ya kara da cewa jami’an sojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindiga har ta kai ga sun tsere sun bar maboyar su.

Janar Danmadami ya ce bayan tserewar mayakan jami’an sun kubtar da mutane uku da yan bindigan su ka yi garkuwa da su.

Kazalika Danmadami ya ce a yayin sumamen dakarun sun kuma kwaso makamai da su ka hada da bindiga kirar AK47 guda biyar babura 30 da sauran wasu kayayyakin.

Bayan samun nasarar rundunar ta sojin ta jinjinawa jami’an da su ka yi namijin kokarin tare da kara musu karfin gwiwa da kuma yin kira ga al’umma da su sanarwa da jami’an dukkan wani abu da ba su yadda da shi ba a yankunan nasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: