Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Fatakwal din Jihar Rivers ta soke takarar wasu ‘yan takara na Jam’iyyar APC a mazabu 16 na Majalisar Dokokin Jihar.

Kotun ta dauki matakin hakan ne sakamakon rashin sanya idanu da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ba ta yi ba a yayin gudanar da zaben ‘yan takarar da jam’iyyar ta gudanar a mazabun.

Bayan kammala zaben da aka gudanar jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar ta Rivers ta shigar da kara gaban kotun dangane da saba ka’idoji da jam’iyyar ta yi a yayin zaben.

Bisa yankin hukuncin da kotun ta yanke jam’iyyar ta APC ta rasa kusan rabin ‘yan takarar na Majalisar ta Dokokin Jihar wanda za ta gudanar da takarar a mazabu 16 a zaben shekarar 2023 mai gabatowa.

Mai magana da yawun jam’iyyar na Jihar Sogbeye Eli ya nuna rashin jindadin sa dangane da hukuncin da kotun ta yanke,inda ya ce hukumar ta INEC ta gabatar wa da kotun hujjoji sannan kuma ta sanya idanu a yayin zaben ‘yan takarar.

Kakakin ya ce koda wane lokaci jam’iyyar za ta iya daukaka kara akan hukuncin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: