Wasu ‘yan bindiga a Jihar Nasarawa sun yi garkuwa da wasu mutune matafiya 19 a lokacin da su ke tsaka da tafiya akan hanyar su ta zuwa Abuja daga Jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a daren Jiya Juma’a a lokacin da ‘yan bindigan su ka tare kan hanya a yankin Eggon da ke Jihar Nasarawa.

Matafiyan da ‘yan bindigan su ka yi garkuwa da su sun hada da mata da yara a cikin motar wadda takasance ta haya.

A lokacin da maharan su ka tare motar su ka nufi da su cikin daji ciki harda direban motar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar ta Nasarawa Mai-yaki Muhammad Baba ya tabbatar da faruwal lamarin inda ya ce sun aike da jami’an su gurin cikin dajin domin kubtar da mutanen.

Mai-yaki ya ce da misalin karfe shida na safiyar yau Asabar su ka aike da jami’an nasu da kuma ‘yan sakai domin su ceto mutanen.

Bayan yin garkuwa da matafiyan maharan sun kira ‘yan uwan mutane inda su ka nemi da su biya kudin fansa kafin su sako mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: