Ministan Makamashi na Najeriya Abubakar Aliyu ya bayyana cewa shirye-shirye sun fara nisa na kara karfafa hanyoyin samar da wutar lantarki a birnin tarayya Abuja da kewayen ta.

Ministan ya sanar da hakan ne a yayin zantawar sa da ‘yan jaridu bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai gurin aikin a ranar Juma’a.
Abubakar Aliyu ya bayyana cewa aikin da za a gudanar zai kara karfafa wutar ta Lantarki wadda kamfanin TCN yake samarwa a yankin da megawat 1,000.

Aliyu ya kara da cewa kamfanin na TCN shine wanda gudanar da aikin.

Kazaliza Abubakar Aliyu ya ce kungiyar taimaka wa kasashen gwamnatin Faransa AFD itace ta dauki nauyi yin aikin.
A yayin kammala aikin anasaran zai kara karfin lantarkin wanda kuma hakan zai sa a karawa tasoshin wutar lantarki na Dawaki Apo Kuje Wumba da kum Lugbe.
Ministan ya kara da cewa bayan an kammala gudanar da aikin za a kaddamar da shi a watan Disamba mai kamawa.