Hukumara zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa, bata binciken Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

A sanarwar da Shugaban kwamitin Yada labarai da ilimantar da masu zabe na Hukumar Festus Okoye ya fitar a jiya Asabar, ya bayyana cewa labaran da suke yawo akan cewa hukumar zata binciki Tinubun na karya ne.

Ya kuma kara da cewa, wasu ne kawai suka kirkiri Labarin kanzon kurege suke yadawa Dan wata manufa tasu ta daban.

Idan za’a iya tunawa akwai Labarin da yake ta bazuwa tun ranar juma’a a kafafen sadarwa, Inda aka bayyana cewa Hukumar INEC din tana binciken Dan takarar na Jam’iyyar APC Tinubu.

A sanarwar bogin da aka fitar an bayyana cewa Hukumar tana binciken Tinubun ne, akan wata badakala da gwamnatin Amurka a shekarar 1993 bisa zargin binciken sa da akeyi akan safarar miyagun kwayoyi.

Saidai acikin sanarwar dai ta Okoye yace, wannan Labarin ba daga Hukumar zaben ta INEC ya fito ba kuma basu San daga inda yake ba, wasu ne dai kawai suka kirkiro shi.

A karshe Festus Okoye din ya kara da cewa, sanarwar da Hukumar INEC take fitarwa ana dorawa ne a shafin labaran ta na yanar gizo, a lokaci guda kuma ya bazu zuwa sauran sassan kafofin sanarwar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: