Siyasa
Bama Yin Bincike Akan Tinubu – INEC
Hukumara zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa, bata binciken Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.
A sanarwar da Shugaban kwamitin Yada labarai da ilimantar da masu zabe na Hukumar Festus Okoye ya fitar a jiya Asabar, ya bayyana cewa labaran da suke yawo akan cewa hukumar zata binciki Tinubun na karya ne.
Ya kuma kara da cewa, wasu ne kawai suka kirkiri Labarin kanzon kurege suke yadawa Dan wata manufa tasu ta daban.
Idan za’a iya tunawa akwai Labarin da yake ta bazuwa tun ranar juma’a a kafafen sadarwa, Inda aka bayyana cewa Hukumar INEC din tana binciken Dan takarar na Jam’iyyar APC Tinubu.
A sanarwar bogin da aka fitar an bayyana cewa Hukumar tana binciken Tinubun ne, akan wata badakala da gwamnatin Amurka a shekarar 1993 bisa zargin binciken sa da akeyi akan safarar miyagun kwayoyi.
Saidai acikin sanarwar dai ta Okoye yace, wannan Labarin ba daga Hukumar zaben ta INEC ya fito ba kuma basu San daga inda yake ba, wasu ne dai kawai suka kirkiro shi.
A karshe Festus Okoye din ya kara da cewa, sanarwar da Hukumar INEC take fitarwa ana dorawa ne a shafin labaran ta na yanar gizo, a lokaci guda kuma ya bazu zuwa sauran sassan kafofin sanarwar su.
Labarai
Yadda Kawu Sumaila Ya Bayar Da Tallafi A Makarantu Da Asibitoci A Kano Ta Kudu
Sanata Kawu Sumaila ya bayar da tallafin Kujerun Makaranta Sama da 3,000 da gadon kwanciyar marasa lafiya a asibiti guda 1,000.
Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya aiwatar da wannan babban kokarin daga darajar mazabarsa inda ya bayar da tallafin kujeru da teburan karatu sama da dubu uku da gadon kwanciyar marasa lafiya a asibiti har guda1000 da katifu.
An gudanar da taron bayar da tallafin a unguwar Tokarawa a ranar asabar data 20 ga watan Oktoba, 2024, wanda hakan ya tabbatar da manufar sa ta son magance matsalar karancin ilimi da kiwon lafiya a yankin Kano ta Kudu.
Gudunmawar, wacce ta kasance wani bangare na shirye-shiryen samar da ayyukan cigaban mazabar Kano ta Kudu, Sanata Sumaila, yana da nufin habaka cibiyoyin ilimi da ayyukan kiwon lafiya a yankin.
Sanata Sumaila, yace manufar bayar da tallafin itace a samar da ingantaccen yanayin koyo ga dalibai da kuma inganta kula da marasa lafiya a fadin Kano ta Kudu.
Ya kuma jaddada cewa, wannan shi ne mafarin kokarinsa na kawo sauyi ga muhimman sassan lafiya da Ilimi a mazabar tasa.
Sanata Kawu Sumaila ya kara da cewa a matsayi sa na wakili aikin sa ne tabbatar da cewa makarantun yankin da asibitoci sun samu abubuwan da suke bukata wajen gudanar da aiki ba tare da tangarda ba.
Haka zalika ya roki wadanda aka bawa tallafin suyi amfani da shi ta kyakyawar hanyar da al’ummar Kano ta kudu zasu cigaba da cin moriyar kayan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya halarci taron, ya yabawa kokarin da Sanata Kawu Sumaila ke yi, inda ya bayyana cewa irin wannan gudumawa na da matukar muhimmanci ga ci gaban jihar Kano baki daya.
Gwamna Abba yace ana kyautata zaton wannan tallafi zai inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, musamman rage yawan mata masu juna biyu da suke rasa ransu lokacin haihuwa a fadin Jihar Kano.
Sanata Kawu Sumaila ya kuma bayar da tallafin karatu ga dalibai sama da 600, masu karatun bangaren kimiyya, da nufin tallafa wa iliminsu da kuma gudunmawar da za su bayar a fannin kiwon lafiya a nan gaba.
Siyasa
An Fara Zaɓen Shugabannin Kananan Hukumomi A Kaduna Da Kogi
A yau ake gudanar da zaben shuwagabannin kananan hukumomi a jihohin Kaduna da Kogi.
A jihar Kaduna jam’iyyar 10 ne su ka shiga zaben.
Akwai masu neman kujerar shugabannin kananan hukumomi guda 79 wadanda su ka shiga zaben
Shugaban hukumar zabre mai zaman kanta a jihar Farfesa Joseph Gambo ne ya shaida haka.
Sai dai gwamna Uba Sani na Jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar su ce za ta lashe dukkanin kujerun.
Batun da ya hifar da cecw kuce.
A jihar Kogi ma ana gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a yau.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewar za a gudanar da zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Labarai
Ba Zan Ce Uffan Kan Rikicin NNPP Ba – Kwankwaso
Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ba zai tsoma baki a kan rikicin cikin gida da ya kunno kai a jam’iyyar su ta PDP ba.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da ƴan jarida su ka yi masa tambaya a gidansa da ke Kano.
Ya ce bai kamata ya saka baki a kan rikicin ba a don haka ba zai ce komai a kai ba.
A jiya ne dai shugaban jam’iyyar ya sanar da dakatar da saataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri Muhammad Dugwal.
Sai dai daga bisani gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewar ya yi sasanci dangane da rikicin.
A wani bidiyo da ke yawo an hango Baffa Bichi na nisanta kansa daga zargin da ake masa na kirkirar wani bangare daga cikin jam’iyyar NNPP.
Ko da dai jam’iyyar ba ta fito karara ta bayyana dalilin da ya sa ta dakatar da su ba.
-
Labarai10 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari