Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya rabawa marayu mutum 200 tallafin Naira Miliyan Goma. Wadanda aka zabo daga sassa daban-daban na kananan hukumomin Jihar.

Marayun dai an bawa kowannen su kimanin Naira Dubu Hamsin, kuma an zakulo su ne daga kananan hukumomi 17 da suke Jihar Ta Yobe.
Lokacin da yake gabatar da tallafin Buni ya bayyana cewa, ya kamata a dinga tallafawa marayu Dan Samar da Al’umma ingantacciya kuma Ta gari.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa, Gwamnatin sa tana kula da halin da marayu suke ciki da sauran marasa karfi kuma tana ganin wajibinta ne ta nuna kulawa a garesu.

Sannan kuma a gefe daya, Buni ya godewa Gidauniyar Tallafawa Marasa karfi ta Qatari akan irin tallafin da suke bawa marayu suma, da kuma kayayyakin tallafin da suke rabawa sauran Al’umma mabukata.
Shugaban shirin kuma mai bawa gwamnan shawara akan harkokin Addinai Ustaz Babagana Mallam Kyari, shima ya yabawa Gwamnan bisa kulawarsa ga marayu da Zaurawa a fadin Jihar ta Yobe.