Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa a Najeriya ta ce babu takaimaiman ranar da za a koma jigilar mutane daga Kaduna zuwa Abuja.

Darakta a ma’aikatar Fidet Okhiria ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce hukumar ba ta tsayar da ranar da za a koma jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna ba.

Daraktan ya musanta labaran da su ke yawo cewar za a koma bakin aiki a ranar 24 ga watan Nuwamban da mu ke ciki.

Ya ce hukumar na shirin ganin an koma jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna, sai dai ba a tsayar da ranar da za a koma bakin aiki ba.
Hukumar ta dakatar da jigilar mutane tun bayan da aka yi garkuwa da wasu mutane yayin da wasu su ka rasa rayuwarsu a farkon shekarar da mu ke ciki.