Shahararren Dan wasan kasar Portugal kuma Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa, baya mutunta mai Horarwa Erik Ten Hag saboda shima baya mutunta shi.

A wata Tattaunawarsa da Dan Jarida Piers Morgan Ronaldo ya bayyana cewa, Mai Horarwar Na Manchester baya girmama shi, Duk kuwa Wanda baya girmama shi shima bazai mutunta shi ba.

A cikin Hirar dai Ronaldo ya kara da cewa, yana son Kungiyar ta Manchester da magoya bayanta kamar yadda suma suke kaunarsa. Amma fa idan kungiyar tana son cigaba dole ne sai sun canza abubuwa da yawa.

Kuma ya kara da cewa, Manchester din sun yaudare shi kuma sun so su tursasa cire shi daga kungiyar tun kakar wasan da ta gabata, ba iya mai horarwa ba har da sauran wadanda suke kewaye dashi.

Ronaldon dai ya kuma cewa, yana son cigaban kungiyar shine ma dalilin da yasa yazo, amma akwai wasu abubuwan da ake yi da basa taimakawa kungiyar zuwa babban mataki kamar kungiyar Manchester City, Liverpool da kuma Arsenal a yanzu.

Ya kuma kara da cewa, tun da ya bar kungiyar a baya babu abinda ya canza kama daga wajen wanka har da wurin motsa jiki, lokacin da ya dawo ya dauka zai ga wani cigaba amma sai ya ga abinda ya bari tun a shekaru ashirin baya.

Idan za’a iya tunawa dai Alaka tayi tsami tsakanin Ronaldo da Mai horarwa Erik Ten Hag tun a wasansu da kungiyar Tottenham, bayan da Ronaldo ya fice daga filin kafin a tashi daga wasa.

Dalilin da yasa kenan aka hukunta shi ta hanyar mayar dashi daukar horo karamar kungiya da kuma ajiye shi a wasa Na gaba da suka fafata.

Wannan dambarwar ce ta sa ake tunanin Dan wasa Ronaldo ka iya Barin kungiyad a watan musayar ‘yan wasa Na Janairu mai gabatowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: