Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ba da umarnin a biya baki ɗaya ma’aikatan jihar albashinsu na watannin Nuwamba da Disamba kafin ranar 10 ga watan Disamba, 2022.
Manema labarai tattaro cewa bayan haka gwamnan na jam’iyyar APC ya yi umarnin a ƙara wa kowane ma’aikaci da N15,000 a matsayin kyauta.
Yace gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa ma’aikata isasshen lokaci da kuɗaɗen da zasu shirya zuwan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Sanarwar ta ce a kokarin gwamnatin Ebonyi na ganin walwala a fuskokin ma’aikatanta, gwamna Dave Umahi, ya ba da umarnin nemo ƙarin buƙatu daga bankuna.
Buƙatun sun ƙunshi tabbatar da an biya ma’akatan jiha da na kananan hukumoni albashinsu na watannin Nuwamba da Disamba tare da Bonus ɗin Kirsimeti N15,000 daga nan zuwa 10 ga watan Disamba.
Mista Oko ya ƙara da cewa wannan garaɓasa da gwamna ya gwangwaje ma’aikata da shi sun yi dai-dai da sauran kyaututtukan da ya saba kamar Buhun Shinkafa da sauransu.