A safiyar yau Talata ne dai aka samu tashin Gobara, a Kasuwar Singa da take Jihar Kano a Arewa Maso Yammacin Najeriya.

An bayyana cewa Gobarar ta tashi ne, tun kimanin bayan karfe Tara Na safiyar yau Talata din.
Wani Rumbin adana abubuwan ciye ciye Na Biskit da Alewa, shine aka ga katsam ya kama da wuta a cikin Kasuwar.

Jami’an Hukumar Kashe Gobara tun suka bayyana, kuma yanzu haka suna iyaka kokarin su Dan ganin sun shawo kan matsalar wutar da take ci.

Gobarar dai ta kama ne a wani Gida da yake dauke da Rumbunan Ajiyar, Wanda aka bayyani shi da sunan Kamfanin hada hadar kasuwanci Na Mimza.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyyana cewa, ba’a San makasudin faruwar gobarar ba amma an fi tunanin Matsalar wutar lantarki ce ta jawo.
Kasuwar Singa dai Babbar kasuwa ce a Jihar Kano ta hada hadar kasuwanci, musamman kayayyakin da suka hada da Abubuwan Mayan abinci da makamantansu.