Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai nemi a yafewa Najeriya bashin da ke kanta na kasashen waje idan ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin da yake magana kan shirinsa na farfado tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, shirinsa na mai da bangarori da dama hannun ‘yan kasuwa zai samarwa ‘yan Najeriya aikin yi.

Atiku ya yi wannan batu ne a wani taron tsoffin daliban makarantar kasuwanci ta Legas da aka gudanar a yau Talata na shekarar 2022.

Da yake magana game da halin rikicin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a yanzu, Atiku ya ba da misali da nasarorin da PDP ta samu tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

A cewarsa, a wancan lokacin, gwamnatin PDP ta yi nasarar nemawa Najeriya afuwar bashin da ake binta, kana gwamnati ta habaka tattalin arzikin kasar cikin kankanin lokaci ta hanyar hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya kuma fadakar da jama’ar da suka halarci zaman kan lamuran da suka shafi tattalin arzikin kasa, tallafin man fetur, hada-hadar kudade, batun bashi da makamashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: