Dan takarar Shugabancun Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin  idan aka zabe shi zai yi iyakar kokarinsa wajen dorawa kan nasarorin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu.

Ya kuma yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar nan da tsaro da wutar lantarki da harkokin noma da samar da ayyukan yi da bunkasar harkokin masana’antu.

Tinubu ya yi wannan jawabin ne a yayin bikin kaddamar da yakin neman zabensa da ya gudana ranar Talata a babban filin wasa na Rwang Pam da ke Jos babban birnin jihar Filato.

Tsohon Gwamnan Jihar ta Legas ya kuma kira ga ‘yan Najeriya da su lura da ’yan siyasar da za su jefawa kuri’unsu a wannan zabe da za a gudanar tare da yin watsi da marasa cika alkawuran da suka dauka.

Shugaban Kasa Muhammadu Bahari, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kammala dukkan shirye shiryenta na lashe zaben saboda irin dimbin ayyukan alherin da suka shimfida a Najeriya, y Kara da cewa ganin irin goyan bayan da Tinubu ya samu yayin zaben fid-da gwanin jam’iyyar ta APC, ya nuna cewa lallai ya karbu a wajen ’yan Najeriya, sannan Buhari ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar, su tashi su yi aiki don ganin jam’iyyar ta kai ga nasara a zaben.

Shi ma Shugaban jam’iyyar APC n kasa, Alhaji Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyarsu ba ta tsoran kowace jam’iyya a zaben ganin irin nasarorin da aka samu a gwamnatin Shugaba Buhari, idan aka zabi Bola Tinubu, zai dora ne a kan irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na yakin neman zaben na Bola Tinubu kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce Jihar Filato ta shirya irin wadannan tarurrukaa na yakin neman zabe kuma daga bisani ’yan takarar su lashe zaben a shekara mai zuwa

Shi dai wannan taro, ya sami halartar Gwamnonin jam’iyyar ta APC da ’yan majalisar tarayya da na jihohi da dubban magoya bayan jam’iyyar, daga dukkan jihohin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: