Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta tabbatar da kama wata mota makare da kwalaben giya a lokacin da motar ke yunkurin shigowa Jihar ta Kano.
Babban Daraktan hukumar Dr Harun Ibn Sina ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke ganwa da manema labarai a harabar hukumar.
Dr Harun ya bayyana cewa motocin sun iso kano ne daga garin Zariya inda su ka kasan ce guda uku.
Ibn Sina ya ce sun samu nasarar kama guda daya inda su ke ci gaba da binciken domin gano sauran biyun da zarar sun shigo garin na Kano.
Kwamandan ya kara da cewa kowacce kwalba da ke cikin motar cike take da giya.
Dr Harun Ibn Sina ya ce dokar haramta amfani da giya ta Jihar Kano ta na ammafani karkashin sashi na 401 wanda kuma sashin kekan cewa sayar da giya ko Tallanta ko shanta a Kano haramun ne.