Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna sun samu nasarar kama wani dan bindiga bayan wata musayar wuta da su ka yi da su a Kauyen Madugu da ke kan hanyar Galadima wa zuwa Tunburtu cikin karamar hukumar Giwa ta Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Muhammad Jalige shine ya shaida hakan.

Jalige ya ce jami’an ‘yan sandan sun kama dan bindigan ne a ranar Alhamis tare da kwace babura guda biyar na ‘yan uwansa ‘yan bindigan bayan sun tsere daga bude musu wuta da ‘yan sandan su ka yi.

Kakakin ya ce bayananan da su ka samu ne ya sanya su ka tura jami’an tsaro hanyar su ka budewa batagarin wuta har ta kai ga sun tsere.

Jalige ya kara da cewa wanda su ka kama ya amsa dukkan tambayoyin da a kai masa tare kuma da ajiye kayan da aka kama a Ofishin na yan sanda.

Daga bisani kuma Jalige yayi kira ga mazauna kauyen da su sanar da jami’an tsaro dukkan wanda su ka gani jikinsa dauke da raunin harbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: