Labaran jiha
Gwamnan Jihar Ribas Ya Kaddamar Da Wasu Ayyuka Da Yayi A Jihar
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a daren Lahadi ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, a Birnin Fatakwal, babban birnin jihar, gabanin kaddamar da titin Mgbutanwo da ke karamar hukumar Emohua a yau Litinin.
Wike ya gayyaci ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa bude ayyukansa daban-daban a Ribas, ya ce ya gayyaci ‘yan siyasa daga Jam’iyyun adawa don bude ayyuka a jiharsa domin su gani da idonsu su kuma shaida wa ’yan jam’iyyunsu.
Tsohon shugaban jam’iyyar (APC) a kasa, Adams Oshiomhole a ranar Larabar da ta gabata ya kaddamar da gadar sama ta 8 a jihar da ke kan titin Ada George, cikin karamar hukumar Obio-Akpor.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kaddamar da gadar sama ta 9 a babbar mahadar
Ikoku a ranar Alhamis.
Hakazalika, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya a Fatakwal ranar Juma’a.
Kusan kimanin watanni, Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da aka fi sani da ‘Yan G5 suna neman shugaban Jam’iyyar, Iyorchia Ayu da ya yi murabus, su na masu cewa bai kamata ‘yan Arewa su zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa ba daga yankin ba.
Sai dai kuma, Ayu, dan asalin jihar Benue, ya dage kan cewa ba zai sauka ba har sai karshen wa’adinsa na shekaru hudu sun cika.
Yayin da ‘Yan G5 din su ka gindaya sharadin sai ya yi murabus a matsayin wani sharadi na goyon bayan Atiku Abubakar, a zaben 2023.
Labaran jiha
Gwamnatin Jihar Kano Ta Soke Komawa Makaranta Ranar Litinin
Gwamnatin jihar Kano ta soke komawar ɗalibai makaranta ranar Litinin.
Hakan na kunshe a wani sakon murya da kwamishinan ilimi a jihar Umar Haruna Doguwa ya sanar.
Ya ce an dakatar da komawa makarantar ne saboda wasu abubuwa dasu ka taso.
Sannan ya ce za a sanar da ranar komawa nan gaba kaɗan.
Kwamishinan ya bai wa iyaye hakuri dangane da jinkirin da aka samu.
Labaran jiha
Ambaliyar Ruwa – Mutane 20 Sun Mutu A Yobe
Mutane 20 ake fargabar sun mutu yayin da mutane 3,000 su ka rasa muhallinsu a jihar Yobe.
Shugaban ƙaramar hukumar Bade Babagana Ibrahim ne ya bayyana haka ya ce lamarin ya faru sakamakon ruwan kamar da bakin ƙwarya.
Ya ce gwamnatin na ƙoƙarin samar da kayayyakin agaj kamar abinci, magunguna, da taftataccen ruwan sha don kare su daga kamuwa daga cutuka.
Sai dai ya ce akwai buƙatar agajin gwamnatin tarayya duba ga yawan masu gudun hijirar.
Shugaban ya ce makonni biyu kenan aka shafe ana samun ruwan sama wanda ya yi sanadiyyar ambaliya.
Lamarin ya shafi Gashua tare da umartar mutanen da ke rayuwa a wuraren da ambaliyar na iya shafa da su kauce tare da barin gidajensu.
Labaran jiha
Bayan Ɓarkewar Zanga-zangar Kan Tsadar Man Fetur Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Umarnin Fito Da Manyan Motoci Da Ɗaukar Mutane Kyauta
Gwamnan jihar Kwara Abdurrahman Abdurrazak ya bayar da umarnin fitar da motoci a kwaryar birnin jihar don saukaka harkar sufuri.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan da jama’a ke kokawa danane da tashin farashin man fetur a ƙasar.
Babban sakataren yaɗa labaransa Rafiu Ajakaye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce za a ɗauki mutane zuwa manyan wurare kyauta
Wannan dai na zuwa ne yayin da masu ababen hawa su ka tafi yajin aiki sanadin ƙarin farashin mai wanda hakan y sa fasinjoji su ka yi cirko cirko a tituna.
Gwamnan ya bai wa jama’ar jihar hakuri dangane da halin da ake ciki na tsadar man fetur.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari