Akalla mutane Goma ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hatsari da ya rutsa da su bayan motar su ta fada cikin ruwa a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

Jami’in hulda da jama a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Yusif Abdullahi shi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar lakacin da wata mota dauke da fasinjoji ta fada cikin ruwan fade dake Gwarzo.
Ya ci gaba da cewa motar wadda kirar Golf ce ta kwacewa direban a dalilin tayar mota da fashe ta kuma ta fada cikin ruwan lakacin da su ke tafiya akan hanyarsu ta zuwa katsina.

Sannan ya ce cikn taimakon Allah sun samu nasarar tseratar da mutane uku a raye da taimakon musunta.

Saminu Abdullahi ya ce mutane Goma sun rasa rayukansu a yayin lamarin da ya faru.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya sai da mutane da dama su ka rasu lakacin da jirgin ruwan ya nutse a karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.