Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi a Najeriya.

Takardun kudin an kaddamar da su ne a yau Laraba a taron majalisar zartarwa na kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kudaden da aka sabunta sun hada da naira 200, 500 da kuma naira 1,000

Da yake jawabi akan sabunta takardun kudin, shugaba Muhammadu Buhari ya ce hakan zai taimaka wajen rage radadin matsi da ake fama da shi , tare da kawar da cin hanci da rashawa.

Sannan ya ce wannan kokari zai kara habaka tattalin arziki da sake daga darajar kudaden Najeriya a idon duniya.
Har ila yau shugaban kasar ya ce wannan aiki zai taimakawa babban banki kasa CBN wajen tabbatar da dokoki da tsare-tsarensa.
Sannan ya yi kira ga alummar Najeriya da su karbi wannan sabon tsari na sauya fasalin kudin a fadin kasar.
A jawabinsa, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya gargadi yan Najeriya kan cigaba da rike tsofaffin takardun kudaden, inda ya ce ranar 31 ga watan Janairu na sabuwar shekarar 2023 ita ce rana ta karshe da za a daina amfani da tsoffin kudaden.
Hukumar zabe a Najeriya ta ce dokokin kundin tsarin mulkin kasar ba su ba ta damar ta ci gaba da yin aikin rijistar kada kuria ba kafin babban zabe na shekarar 2023.
A jiya Talata ne dai rahotanni suka ambato cewa wata babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci hukumar ta ci gaba da aikin rijistar har zuwa kwana 90 kafin zabe.
Hukumar ta INEC ta rufe aikin rijistar zaben tun a watan Yuli da ya gabata, abin da ya jawo martani da koke-koke daga kungiyoyin farar hula cewa za a tauye wa miliyoyin yan kasa hakkinsu.
Amma da yake magana ta cikin shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels , kwamishinan wayar da kan masu zabe na hukumar ta INEC Festus Okoye ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin kotun ba.
Zuwa yanzu dai kwanaki 93 su ka rage a gudanar da zabubbaka a Najeriya.
Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta rahoton da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da ke bayyana cewa jihar ita ce tafi kowacce talauci a Najeriya.
Gwamnatin ta fadi hakan ne a matsayin martani ga rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta fitar kwanan nan, wanda ya nuna jihar Sakkwato ce ta fi fama da talauci a kasar.
Gwamnatin jihar ta mayar da martanin ne ta hannun babban sakataren maaikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar, Alhaji Arzika Bodinga.
Bodinga ya bayyana haka ne sailin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na yini daya da aka shirya a jihar.
A makon da ya gabata ne hukumar kididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa yan Najeriya miliyan 133 ke fama da talauci.
Sannan daga cikin jihohin kasar nan, jihar Sakkwato ta kere kowace jiha fama da matsanancin talauci.
BREAK:
Masu kallo kar ku shaafa kuna kallon labaran ne daga nan gidan talabijin na jaridar matashiya. Haka zalika za ku iya bibiyarmu don cigaba da kallon shirye shiryenmu a shafukan sada zumunta na zamani wato Facebook, Instgram, Youtube da sunan Mujallar Matashiya ko kuma a Twitter mai suna @mmatashiya.
Bari mu karbi wannan sako da zarar mun dawo labaran za su dora.
Barkanmu da dawowa.
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a kan dokar inganta rayuwar masu bukata ta musamman , wadda majalisar dokokin jihar ta zartar kwanan nan.
Gwamnan ya ce dokar za ta taimaka wajen sanyasu cikin tsare-tsaren gwamnati da suka shafi cigaban kasa.
Sannan gwamnan ya kara da cewa wanzuwar dokar ta inganta rayuwar mutanen za ta ba da damar fito da wannan bangare na alumma da nauoin bukatunsu ta yadda za a shigar da su a cikin tsarin gwamnati , tare da share musu hawaye.
Dokar dai ta hana yi musu kallon kaskanci, sannan ta yi tsari na saukaka musu rayuwa wajen shige da fice a gine-gine da maaikatun gwamnati, ga kuma tanadin da aka yi musu na wani kaso a guraben aiki.
Malam Yarima Sulaiman Ibrahim na cikin shugabannin masu bukata ta musamman a Najeriya, kuma daya daga cikin jagororinsu a jihar Kano, wanda ya ce suna murna, sakamakon sanya hannu a dokar da gwamna ya yi.
Majalisar dattijai ta yi sammacin ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmad, don ta yi musu bayanin a kan kudi kimanin naira Biliyan 206 da aka saka a cikin kasafin kudi shekarar 2023 na maaikatar jin kai da kula da walwalar alumma.
Kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattijai sun bukaci ministar ne da ta zo don yi musu bayani, a kan makudan kudade da aka sa duk da halin karancin haraji da matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi a wannan lokaci.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa bukatar gayyatar ministan ta samo asali ne, a lokacin kare kudin maaikatar jin kai da kula da walwalar alumma.
Biyo bayan kasa bayar sahihin bayani da ministar maaikatar Sadiya Umar Faruk ta yi a kan kudaden , Sadiya ta bayyana cewa ba ta san ta yaya aka yi maaikatar kudin ta saka kudaden a cikin kasafin kudin maaikatarta a shekara mai kamawa ba.
Wata kotun daukaka kara mai zamanta a jihar Sakkwato ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar game da soke zaben fidda gwanin gwamna da aka gudanar a jihar Zamfara.
Mai sharia Shuaibu Muhammad ya ce daukaka karar da jamiyyar PDP ta yi bai da makama don haka ilahirin alkalan kotun sun amince da tabbatar da hukuncin baya.
Sannan alkalin ya yi Karin haske da cewa , dan takarar jam’iyyar PDP Lawal Dauda Dare bai da hurumin daukaka kara kan hukuncin da a baya ya amince da shi.
Haka zalika, kotun ta umarci jam’iyyar PDP ta biya tarar naira 100,000 bisa bata lokacin kotu.
Tun da farko dan takarar gwamna na jamiyyar PDP, Ibrahim Shehu ya kalubalanci abokin takarar ta sa Lawal Dare a nasarar da yayi a zaben fidda gwani na gwamna a jihar ta Zamfara.
Shehu na zargin an yi murdiya a zaben fidda gwanin tare da saba kaidojin zabe wanda INEC ta shar’anta.
Sai dai ganin bai gamsu da zaben ba, ya tunkari kotun tarayya mai zamanta a Gusau, kuma ta rusa zaben tare da ba da umarnin a sake shi cikin kwanaki 14.