Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi a  Najeriya.

Takardun kudin an kaddamar  da su ne a yau  Laraba a taron majalisar zartarwa na kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kudaden da aka sabunta sun hada da naira 200, 500 da kuma naira 1,000

Da yake jawabi akan sabunta takardun kudin, shugaba Muhammadu Buhari ya ce hakan zai taimaka wajen rage radadin matsi da ake fama da shi , tare da kawar da cin hanci da rashawa.

Sannan ya ce wannan kokari zai kara habaka tattalin arziki da sake daga darajar kudaden Najeriya  a idon duniya.

Har ila yau shugaban kasar ya ce wannan aiki zai taimakawa babban banki kasa CBN wajen tabbatar da dokoki da tsare-tsarensa.

Sannan ya yi  kira ga alummar Najeriya da su karbi wannan sabon tsari na sauya fasalin kudin a fadin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: