Fasinjoji 17 dake hanyar zuwa jihar Legas Sun kone ƙurmus a wani hatsarin Mota da ya auku a babban Titin Abuja-Lokoja da Safiyar yau Talatan.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa mutane huɗu daga cikin Fasinjojin waɗanda suka taso daga jihar Gombe, Allah ya sa da sauran numfashinsu a gaba sun tsira da saurukan wuta.

Rahotanni sun nuna cewa Jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) sun ɗauki mutanen da hatsarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Abaji domin kula da su.

Wani shaida, Kabir Garba, yace hatsarin ya rutsa da wata Motar Bas Toyota Hiace mai ɗaukar mutum 18 da lambar Rijista GME 20 XA da kuma Babbar Tirela Daf mai lamba BAU 632 XA.

cewarsa, Motocin sun yi karo da juna a kusa da Yaba junction da ke kan babban Titin Abuja zuwa Lokoja.

Yace Motar Bas ɗin wacce ta fito daga Titin Abuja-Gwagwalada da gudun tsiya, ta bugi Tirelar ta baya kana ta tarwatse filla-filla.

Wakilin jaridar wanda ya dira wurin da misalin karfe 7:23 na safe ya gano cewa Jami’an kwana-kwana na fafutukar kashe wutar yayin da dakarun FRSC ke kokarin zaro gawarwakin da suka ƙone.

Leave a Reply

%d bloggers like this: