Yan sandan jihar Kaduna sun ceto matafiya 76 da aka yi garkuwa da su a hanyar Funtua zuwa Zaria a unguwar Gulbala a karamar hukumar Giwa ta jihar, ta hanyar hadin gwiwa da sojoji.

Kakakin rundunar ‘yansandan, DSP Mohammed Jalige, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Juma’a, bayan rahoton da aka samu daga hedikwatar ‘yansanda a karamar hukumar Giwa.

A cewarsa, rundunar ‘yansandan ta samu rahoton ‘yan bindiga da dama ne suka tare hanya, kuma a cikin haka ne suka yi awon gaba da fasinjoji da dama, zuwa inda suke.

Ya bayyana cewa, rundunar ta tattara jami’an tsaro ciki har da sojoji, inda suka shiga wurin, kuma suka gano wata motar da babu kowa a ciki – wata motar kirar Ford mai dauke da lamba APP 667 XG, ta ce ta dauki fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Rundunar ta ce sojojin sun kara tarwatsa duk wani shingen hanya, tare da yin artabu da ‘yan bindigar tare da samun nasarar ceto dukkan mutane 76 da lamarin ya rutsa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: