Gwamnatin Burtaniya ta ce miyagun ‘yan siyasa a Najeriya su kwana da sanin cewa ba za ta ba su izinin shiga kasarta ba.

Burtaniya ta yi wannan gargadi ne ga ‘yan Najeriya da ke tunzura magoya bayansu wajen ta da hankali ko kuma rikici da ke kai ga rasa rayuka, lura da yadda irin wadannan matsaloli ke yin barazana ga zaben shekara ta 2023.

Babbar jami’ar diflomasiyyar kasar Catriona Laing ta bayyana haka lokacin da ta jagoranci tawagar manyan jami’anta domin ganawa da shugabannin kwamitin zartarwa na jam’iyyar adawa ta PDP.

Laing ta ce zaben shekarar 2023 na da matukar mahimmanci ga Afirka da duniya baki daya, saboda haka hankalin Burtaniya da na kasashen Duniya ya karkata akan kasar.

Jami’ar ta ce Burtaniya ta yi matukar damuwa da irin laifukan da ke da nasaba da zabuka 52 da aka gani a jihohi 22 daban-daban, ciki har da harin da aka kaiwa tawagar jam’iyyar PDP a jihar Borno.

Laing ta ce su na cike da damuwa kan irin wadannan tashe-tashen hankula, saboda haka suka bukaci tattaunawa da shugabannin jam’iyyar kan matakan da ya kamata a dauka domin tabbatar da yin zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.

Jami’ar ta Burtaniya ta kara da cewa yana da matukar wahala mutane su fito suyi zabe matukar su na fuskantar bara zana, wanda hakan ka iya shafar kimar zaben baki daya, Laing ta cigaba da cewa kasar Burtaniya za ta cigaba da sanya ido akan ‘yan siyasar da ke tada hankali tare da tunzura jama’a wajen amfani da kafafen yada labarai a kowacce jam’iyya domin daukar mataki a kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: