Hukumar yaki da cutar Sida a Najeriya ta ce sama da mutum milliyan daya ne ke shan magungunan rage radadin cutar a fadin kasar.

A lokacin wata tattaunawa da manema labarai a birnin Abuja, shugaban hukumar Gambo Aliyu, ya ce hakan na nuna irin cigaban da aka samu a bangaren yaki da cutar, kasancewar mutum kasa da mutum dubu dari takwas da hamsin ne ke shan maganin a shekarar 2017.

Ya kara da cewa yawan masu kamuwa da cutar ya ragu daga 103,404 a shekarar 2019 zuwa 92,323 a shekarar 2021.
Gambo Aliyu ya kara da cewa an sami karuwar cibiyoyin kula da masu cutar kamar yadda a shekarar 2017 akwai cibiya guda 10 yayin da aka samu cibiyar guda 118 a shekarar 2021.

Ya cigaba da cewa ya zuwa yanzu ana kula da masu cutar 221,000 a cibiyoyin kula da masu cutar da ke fadin kasar.

Bayanan na zuwa ne gabanin ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya wanda ake sirin farawa a wannan shekara.

Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire ya ce taken ranar na wannan shekara shine samar da dama ga kowa wajen kula da kuma kare yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki.

Ya ce an fitar da taken ne a matsayin wani sabon yunkuri na takaita yaduwar cutar a fadin duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: