Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana samar da aikin yi a tsakanin matasa da cewar hakan na iya rage matsalar tsaro da kuma samar da cigaba a kasa baki daya.

Sarkin Kano ya bayyana haka ne yayin da ya karbi ziyarar shugabannin cibiyar zayyanar sadarwa wato initution of graphic communication a fadarsa.

Sarkin Kano ya ce samar da aikin yi ab ne da ya dace musamman a wannan lokaci da wasu matasan ke kokarin shiga bangar siyasa.

Ya kuma yabawa shugabannin a bisa samar da cibiyar ganin yadda hakan zai taimaawa jihar ano da ma kasa baki daya.

A nasa jawabiin, shugaban cibiyar Dakta Ibrahim Danjuma ya ce ya samar da cibiyar ne domin nuna kishinsa ga jihar Kano da mma gwamnatin nKano ganin yadda ta ke kokarin talafawa bangaren atasa.

A wani labarin kuma mai martaba sarkin Kano ya amince da nadin Malam Umar Bashir a matsayin limamin mmasallacin garin Rangaza da ke karamar hukumar Ungogo a Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: