Shugaban kasar Guinea-Bissau kuma Shugaban kungiyar ECOWAS, Umaru Sissoco Embolo, ya ce ya zama shugaban kasar Guinea-Bissau ne da taimakon Allah da kuma taimakon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Embolo ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a yayin taron shugabannin Afrika da ke gudana a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.
Shugaban ya ce ko a shekarar da ta gabata sai da su ka sanyawa wata hanya sunan shugaba Buhari.

Embalo ya bayyana shugaba Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba, wanda ya kware wajen yakar rashawa da cin-hanci.
Ya kara da cewa shugaba Buhari jigo ne ga nahiyar Afrika ba iya Najeriya ba.

A nasa jawabin tsohon shugaban kasar Nijar Muhammadu Issoufou ya ce ya yarda da kalaman Jonh Paden mawallafin littafin Salon shugabancin Muhamadu Buhari, wanda yace Buhari yayi suna kan hakuri da amana da kuma mayar da hankali wajen aiki.
Tuni dai Attajirin nan na Najeriya Muhammad Indimi ya dauki nauyin rabawa mahalarta taron kwafi 1000 na littafin mai taken salon shugabancin Muhammmadu Buhari.