Hukumar dake dakile cututtuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya ta bayyana cewa akalla mutane 19,228 ne suka mutu Sakamakon cutar Amai da gudawa a shekarar 2022

Hukumar NCDC ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter a jiya Juma a.

Ta ce cikin shekara Daya an samu yawan mace-mace a Najeriya a dalilin annobar Amai da gudawa.

Sannan rahoton ya nuna cewa jihohi 31 ne aka fi samun masu dauke da cutar a Najeriya.

Kuma cutar Amai da gudawa ta fi tsamari a lokaci irin na damin saboda rashin tsafta da ba a yi.

Jihohin da aka samu yawan mace-macen sun hada da Abia, Akwa Ibom, Adamawa, Anambara, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, kaduna

Sauran su ne kano, katsina, kebbi, kwara, Legas, Nasarawa, Naija, Ondo, Osun, Oyo, Filato, Ribas, Sokoto, Yobe, da kuma zamfara.

Sannan adadin yafi yawa a jihohin arewacin kasar kamar yadda rahoton ya nuna a jimlance.

Sai dai a cikin watan da muke ciki ba samu wani da ya rasu ba a dalilin cutar ta amai da gudawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: