Wata gagarumar Gagarumar gobara ta lashe shaguna dari da hamsin (150) a babbar kasuwar Kachako dake karamar hukumar Takai ta jihar Kano.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya fitar, yace lamarin ya auku da tsakar ranar Litinin.
Ya ce sun sami kiran gaggawa daga hukumar kashe gobara ta yankin wurin karfe 1:13 na rana kuma a take suka tura jami’an ceto wadanda suka isa wurin karfe 1:21 na rana don kashe gobarar dake zagayawa sauran shaguna.

Ya ce ana zargin wutar ta fara ne sakamakon wutar da masu shaye-shaye suka saka wa kasuwar.

Girman farfajiyar kasuwar ya kai kafa 2,000 a fadi da tsayin kafa 1,500 a fadi, Cike da nasara suka tseratar da shaguna 800 daga wutar.
Shaguba 150 ne suka kone tare da asarar dumumbin dukiya mai yawa, saidai ba a sami asarar rayuka ba ko kadan.