Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta ankarar da ‘yan Najeriya cewa sabon rikici zai kunno kai wanda tace sai ya zarce wadanda aka taba yi a jami’o’in Najeriya.

Har zuwa yanzu, ASUU na neman dauki daga masu ruwa da tsaki tare da ‘yan Najeriya masu fadi a ji da su saka baki don Gwamnatin tarayya ta biya mambobinta a fadin kasar nan albashinsu da aka rike na tsawon wata takwas.

Shugaban ASUU na jami’ar Ilorin, Farfesa Mayosere Ajao, ya bayyana hakan a taro na musamman da aka yi a dakin taron jami’ar.

Manema labarai sun rahoto cewa, malaman jami’an sun fita zanga-zanga a cikin jami’ar kafin su koma dakin taron jami’ar inda suka yi jawabi ga manema labarai.

Sun ce duk sun koma bakin aiki a jami’arsu, gwamnati tayi watsi da matsayarsu kan rike musu albashin wata takwas da tayi kan dogaro da tsarin babu aiki, babu biya.

Shugaban kungiyar ya ce ana sanar da jama’a cewa sabon rikici na kunno kai wanda zai zarce duk wadanda aka taba yi a baya, kuma yace mambobin ASUU ba zasu cigaba da aiki kyauta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: