Shugaban hukumar kidaya a Najeriya ya bayyana cewa Najeriya ba ta yin abubuwan da su ka kamata wajen kayyade yawan haihuwa kamar yadda aka tsara.

Nasir Isa Kwarra bayyana hakan ne a Abuja a jiya Talata, lokacin da yake jawabi a yayin taron kasa da kasa kan yawan jama’a a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Haka-zalika shugaban ya ce sam ba a yi abin da ya dace ba , don haka akwai bukatar gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen ganin an lalubo bakin zaren.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu gwamnatin Najeriya na kan gaba a jerin kasashen da ba sa iya samar da abubuwan da matan aure suke bukata na kayyade iyali, inda take da kaso  19 cikin 100.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa hukumarsa isassun kudaden da za ta yi amfani da su wajen samar da kayan tsara iyali a fadin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: