Wata babbar kotu dake birni tarayyar Abuja ta aike da dalibin nan Aminu Adamu Muhammad gidan yari bisa tuhumarsa da yin batanci ga matar shugaban kasa Aisha Buhari.
An gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun yau Laraba.
Lauyan wanda ake zargin CK Agu ya tabbatar wa manema labarai cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban kotu, kuma bai amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.
Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba su ka nemi a bada belin wanda ake tuhuma amma hakan ba ta samu ba.
Har ila yau lauyan ya ce yanzu haka dalibin yana tsare a gidan yarin Suleja kafin kara sauraron bukatar bada shi beli.