Ministoci a kasar Kenya sun yafe albashinsu na wata daya, don amfani da kudin wurin agazawa al’ummar kasar da ke zaune a yankunan da fari ya yi kamari.

Sanarwar da Fadar Shugaban kasar kenya ta fitar ta ce za a saka kudin a gidauniyar da aka kafa don taimakawa al’ummar yankunan da fari ya yi tsanani.
Gwamnatin Kenya ta kuma nuna damuwa kan yadda yan kasuwa ke nuna rashin tausayi wurin tsadar kayan abinci duk da halin da ake ciki.

Miliyoyi al’umma a Kasar Kenya na fama da yunwa inda suke tsananin neman tallafin abinci, yayin da fari ke kara muni a kasar.
