Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da cewa hare-haren kona ofisoshin ta a wasu sassan ƙasar nan ba zai hana gudanar da zaɓen shekarar 2023 ba.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya tabbatar da haka a lokacin da tawagar Jami’an duba Shirye-shiryen Zaɓe na Ƙungiyar Haɗin Kan Afrika, AU su ka kai masa ziyara a ranar Litinin, a Abuja.

Da ya ke bayyana musu abubuwan da su ka faru cikin makonni uku da su ka gabata, Yakubu ya ce INEC za ta sake samar da dukkan kayan da aka lalata a hare-hare uku da aka kai wa ofisoshin su na jihohin Ogun, Osun da Ebonyi.

Makonni  uku da su ka gabata an kai wa ofisoshin INEC hari, aka banka masu wuta a wasu yankunan ƙasar nan, kuma  an lalata wasu kayayyakin zaɓen shekarar 2023 da INEC ta fara rarrabawa a ƙasar.
Sai dai hakan ba zai hana hukumar gudanar da zaɓen 2023 ba.

Sannan kuma duk da wannan lamarin abin damuwa ne matuƙa, wani abin farin cikin shi ne INEC za ta maye dukkan kayan zaɓen da aka lalata.

Wasu masu tada zaune tsaye ne dai suke bin dare su banka wa ofishin Hukumar Zaɓe INEC wuta, kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ne ya tabbatar da faruwar lamuran, cikin wata sanarwar da ya saba fitarwa.

Okoye ya ce daya daga cikin ofishin da aka bi dare aka banka wa wutar ya na garin Iboko, cikin Ƙaramar Hukumar Izzi, ya ce maharan sun banka wa ofishin wuta wajen ƙarfe 10 na dare, inda aka yi asarar kayayyakin zaɓe masu yawan gaske, kakakin ya tabbatar da cewa an ƙone katinan rajistar masu zaɓe, amma ba’a tantance adadin ko guda nawa ne su ka salwanta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: