Jami’an rundunar sojin Najeriya sun hallaka mayakan ISWAP da dama a yayin wata musayar wuta da su ka yi a garin Dambua da ke Jihar Borno.

Jami’an sojin sun hallaka mayakan ne sa’o’i kadan da ‘yan kungiyar ta ISWAP su ka yi mubaya a ga sabon shugaban su Abu Husain Al-kurashi.
Kafin hallaka ‘yan kungiyar sai da su ka kaddamar da wani hari a kauyen Wajiroko da ke Jihar ta Borno.

Wata majiyar sirri ta shaidawa mai sharhi kan sha’anin tsaro Zogazola Makama cewa a lokacin da mayakan na ISWAP su ka isa yankin su ka fara sanya bama-bamai daga bisani kuma su ka koma harbe harbi.

Jami’an sojin sun kwashe kusan mintina 40 su na musayar wuta da yan kungiyar ta ISWAP wanda hakan ya sanya su ka tsere dauke da raunika a jikin su.
Bayan tserewar mayakan na ISWAP wasu jami’an sojin na runduna ta 25 su ka yi musu kwantan bauna tare da hallaka ka su da motocin yakin su biyu.
Daga cikin kayayyakin da jami’an sojin su ka samu nasarar kwaso wa na mayakqn sun hada da bindiga kirar FN guda daya da AK 47 guda biyu da bindigan da ke harbo jirgin sama guda daya da harsasai da kuma gurneti 35 da squran wasu kayayakin.