Rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu ‘yan damfara ta kafar Intanet bayan shan wasu kwayoyi.

Jami’an rundunar sun bayyana cewa lamarin ya farune kusan misalin karfe 12:00 na daren ranar Juma’a a Yenagoa babban birnin Jihar.

Jami’an sun ce matasan sun mute ne a lokacin da su ke tsaka da yin sharholiyar su bayan samun wasu kudade da su ka yi.

Wani mutum wanda ya kasance abokin daya daga cikin mutane ya ce sun rasa ranna su a wani gida da daya daga cikin su ta karbi haya.

Ya ce ana kyautata zaton mutane sun mutune bayan cin wani abinci mai guba da su ka yi.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Benjami Okolo ya tabbatar da mutuwar mutanen inda ya ce mutane sun mutune sakamakon shan wasu kwayoyi da su ka yi.

Kwamishinan ya ce mutanen su biyar ne amma daya daga cikin su bai mutu ba wanda shine ya shaida hakan wanda hakan ne yayi sanadiyyar mutuwar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: