Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani babban masallacin juma’a da ke kan titin Okoroda a Ughelli a Jihar Delta a safiyar ranar Juma’a a Jihar.

Wani mazaunin garin mai suna Larry shine wanda ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce lamarin ya farune da misalin karfen 6:47 na safe a lokacin da mutanen yankin su ke gudanar da sallar Asuba.

Larry ya bayyana cewa zuwan ‘yan bindigan ke da wuya su ka fara harbe-harbe a cikin masallacin wanda hakan ya sanya mutane da ke kusa da gurin su ka tarwatse.

A yayin harin mutane 11 ne su ka jikkata inda mutanen yankin su ka kwashe bayan maharan sun bar cikin masallacin.
Larry ya kara da cewa bayyana kammala kai harin da ‘yan bindigan su ka yi masallan sun shaidawa mazauna yankin cewa maharan sun tafi da mutane uku daga cikin masallatan.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda Jihar Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin ya ce bayan harin jami’an su sun fara gudanar da bincike domin kubtar da mutanen tare da kamo batagarin.