Hukumar Zaɓe mai zaman kanta a Najeriya (INEC), ta ce yanzu haka ta na aiki tare da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), domin magance duk wani cikas ɗin da za a iya fuskanta yayin aikawa da sakamakon zaɓen 2023 ta tsarin yaɗa sakamakon ƙuri’u ta BVAS.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka, ya na mai cewa an fara shiri tun a yanzu domin magance ko da wata matsala za ta bijiro saboda matsalar wuraren da saƙonni ta fasahar zamani ke wahalar isa, wato matsalar ‘network,
Yakubu ya bayyana haka a Legas, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, a ranar Juma’a.

Wannan ƙarin haske da shugaban na INEC ya yi, ya biyo bayan damuwar da wasu ‘yan Nijeriya su ka fara nunawa cewa, za a iya samun matsala da tsarin BVAS a yankunan da ke fama da cikas ɗin samun saƙo ko yaɗa saƙon ta fasahar zamani.

Yakubu ya ce a ranar Talata INEC za ta gana da jami’an hukumar sadarwa (NCC), dangane da yadda za a magance matsalar da ka iya tasowa wajen aika sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da BVAS.
Daga nan sai ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kada su yi fargabar komai dangane da nagartar da zaɓen 2023 zai yi, ta hanyar amfani da BVAS.
Tun da farko sai da Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya roƙi kakafen yaɗa labarai su taimaka wa hukumar zaɓen ta hanyar daƙile bayanan ƙarya da labaran shaci-faɗin da ake dangantawa da INEC.
Ya ce ga shi dai bai fi sauran kwanaki 85 a yi zaɓe ba, amma labaran bogin da ake yaɗawa kan INEC abin damuwa ne sosai.